Wasu yan bindiga da ake zaton yayan kungiyar Boko Haram ne sun kashe jami’an tsaro da kuma wasu ma’aikatan agaji na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) dake aiki a garin Rann dake jihar Borno.
Rann shine hedikwatar karamar hukumar Kala Balge dake jihar Borno a shekarar da ta wuce sai da mutane sama 100 suka mutu a sansanin yan gudun hijira dake garin bayan wani jirgin sojan saman Najeriya ya yi kuskuren jefa bom kan sansanin.
Maharan an ce sun dirarwa garin dauke da muggan makamai.
Wata majiya tace yan ta’addar sai da suka samu nasarar kawar da wani sansanin soja inda suka kashe akalla sojoji hudu.
Yan sanda hudu aka rawaito sun harbe,ya yin da ma’aikatan agaji uku suka rasa rayukansu sauran kuma suka jikkata.
Haka kuma maharan sun yi awon gaba da wata mace ma’aikaciyar jinya.
Samantha Newport jami’ar dake kula da tsaren-tsaren aiyukan jin kai a ofishin UNICEF ta tabbatar da kisan wadansu ma’aikatan agaji.
Newport ta ce dukkanin ma’aikatan agajin yan Najeriya ne.