Boko Haram sun kashe yan sanda hudu da sojoji shida a garin Rann


Yan sanda a jihar Borno a ranar Alhamis sun tabbatar da cewa yan sanda hudu da kuma sojoji 6 aka kashe a harin da kungiyar Boko Haram ta kai a garin Rann dake karamar hukumar Kalabalge ta jihar Borno.

Damian Chuku, kwamishinan yan sandan jihar shine ya bayyana haka lokacin da yake amsa tambayoyi a wurin taron wata-wata a Maiduguri babban birnin jihar.

“A hari na baya-bayannan an karamar hukumar Kala Balge yan sandan kwantar da tarzoma hudu da kuma wasu sojoji shida aka kashe,”Ya ce.

“Yan sanda na cikin yakin da ake yi da ta’addanci domin dawo da zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali kuma an tura su wurare da daban-daban.”

Ya kuma bayyana cewa sama da yan sanda 500 ke aiki a da shirin samar da tsaro na Operation Lafiya Dole ya kuma kara jaddada goyon bayan rundunar domin a samu nasara a yakin da ake da ta’addanci.

You may also like