Boko Haram Ta Kai Harin Bazata Kan Sojin Nijeriya, 13 Sun Raunata, Ba A Ga Wasu Da Dama Ba


nigeria_1
A wani harin samame da mayakan Boko Haram suka kai kan sojojin Nijeriya a yau Talata, a wani sansanin soji  da ke Gashigar, kan iyakar Nijeriya da Nijar, sojoji akalla 13 ne suka raunata a yayin da wasu da dama suka bata kamar yadda kakakin rundunar soja ta kasa Kanal Sani Usman Kuka Sheka ya sanar

Kanal Sani ya bayyana cewa rudanar sojin ta yi iya bakin kokarinta wajen taushe mayakan da suka dirar musu ba zato ba tsammani, amma duk da haka wasu jami’an sojin sun raunata, inda wasu kuma aka neme su aka rasa bayan an gama fafatawar

Kakakin na soji ya bayyana cewa tuni dai aka debe sojojin da suka raunata aka tafi da su don su samu kulawar gaggawa, a yayin da kuma aka shiga neman wadanda ba a gani ba.

You may also like