Boko Haram Ta Sake Kashe Wani Babban Sojan Nijeriya


 

Nijeriya ta kara tafka asara yayin da mayakan Boko Haram suka sake kashe wani babban soja a harin kwantan bauna da suka kai a jiya Litinin.

Laftanal Kanal B.U Umar ya gamu da ajalinsa ne yayin da shi da dakarunsa ke kan hanyarsu na zuwa garin Pritang da ke jahar Yola babban birnin jahar Adamawa, daga garin Bita da ke jahar Borno.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa an budewa hafsan wuta ne lokacin da motar da yake ciki ta taka nakiyan ya kuma fito domin ya duba illar da hakan ya yiwa motar.

B.U Umar shi ne kwamandan bataliya ta 114 (114 TF Battalion) ta sojin Nijeriya, kuma ya karbi mukamin ne makonni uku kawai da suka gabata.

Izuwa yanzu ba a iya tantance adadin wadanda suka rasu ba a harin, amma rahotan ya bayyana cewa an kai mutane 8 asibiti.

You may also like