Ƙungiyar Jama’atu Ahlul Sunna Lidda’awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram ta sako malaman jami’ar Maiduguri 3 da ta yi garkuwa da su.
Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ita ce ta shedawa shugaban kasa Muhammad Buhari sakin malaman su uku waɗanda aka sace a Magumeri dake jihar Borno.
Kungiyar ta Boko Haram ta yi garkuwa da malaman ne bayan wani harin kwanton ɓauna da ta kai wa tawagar wasu ƙwararru dake aikin nemo mai a yankin tafkin Chadji waɗanda ke samun rakiyar jami’an tsaro.
Haka kuma ƙungiyar ta Boko Haram ta sako wasu matan ƴan sanda su 10 da tayi garkuwa da wasu bayan wani hari da ta kai kan ayarin motocinsu dake samun rakiyar jami’an ƴan sanda da soja wajen birnin Maiduguri lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa jihar Adamawa.
An sako mutanen ne bayan da ƙungiyar Red Cross ta kasance mai shiga tsakani.
A cewar hukumar a DSS dukkanin mutanen 13 yanzu haka suna ƙarƙashin kulawar ta kuma za a miƙa su ga iyalinsu da zarar likitoci sun gama dubasu.
Shugaban ƙasa Buhari ya shawarci hukumar kan ta cigaba da ƙoƙarin ƙubutar da ragowar ƴan matan Chibok dake hannun ƙungiyar ta Boko Haram.