Boko Haram ta yi ikirarin kashe sojoji 20 a Arewa maso Gabashin Najeriya


 

 

Kungiyar ta fada a cikin wata sanarwa cewa ta kai farmaki kan wani sansanin hadin guiwa na Najeriya da Nijar da ke a jihar Borno.

Boko Haram Kämpfer (picture alliance/AP Photo)

Kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin kashe sojoji 20 a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya a wani tashin hankali da ya dabaibaye murnar sako wasu daga cikin ‘yan matan Chibok. Kungiyar ta fada a cikin wata sanarwa cewa ta kai farmaki a kan wani sansanin hadin guiwa na Najeriya da Nijar a garin Ghashgahr da ke a jihar Borno. Ta yi ikirarin kashe sojoji 20 da raunata da dama a wani abinda ta kira mummunan fada da ya barke lokacin da ta kai harin a ranar Lahadi. Wani shugaban al’umma a yankin na Ghashgahr ya tabbatar da kai samamen yana mai cewa an yi wa sojojin ba zata lokacin da Boko Haram suka harba gurnati. Shugaban al’umma da ya so a sakaya sunansa ya ce ‘yan Boko Haram sun je yankin cikin motoci guda takwas. Labarin kai harin ya zo ne kasa da mako guda da sakin wasu ‘yan matan makarantar Chibok 21 da ke cikin fiye da 200 da Boko Haram ta yi garkuwa da su fiye da shekaru biyu da suka gabata.

You may also like