Majalisar Dinkin Duniya ta ce hare-haren kungiyar Boko haram yayi sanadin raba kananan yara kimanin miliyan daya a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Rahoton Majalisar Dinkin Duniyar ya kara da cewa, a kalla malaman makarantu 19,000 suka tsere daga arewa maso gabashin Najeriya, yayinda 611 suka rasa rayukansu, sakamakon tashin hankalin da kungiyar Boko Haram ta haddasa daga shekarar 2009 zuwa 2015.
Wani jami’i a sashin yada labaran Majalisar Dinkin Duniyar, Oluseyi Soromekun, ya tabbatar da wannan rahoto wanda za’a wallafa shi a ranar Litinin mai zuwa, a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.
A cewar rahoton hare-haren kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar, ya rusa a kalla makarantu 910, yayinda kuma wasu 1,500 suka rufe bisa tilas.
Hakan ya sa Majalisar Dinkin Duniya bayyana bukatar maida hankali wajen farfado da ilimi a yankin cikin gaggawa, domin a tafi da yankin wajen cimma muradin bunkasa ilimi a nahiyar Afirka nan da shekara ta 2089.