Boko Haram:Sojoji biyar aka kashe, 30 suka bata a hari kan garin Kanamma


Aƙalla sojoji biyar  aka kashe wasu 30 suka bata a wani hari da aka kai kan sansanin soja dake garin Kanamma, hedikwatar ƙaramar hukumar Yunusari ta jihar Yobe.

Kungiyar Boko Haram ake zargi  da kai harin.

Wata majiya mai tushe  dake cikin jami’an tsaro ta shedawa wakilin jaridar Daily Trust cewa  gawarwakin soja biyar aka gano a wurin da aka kai harin.

“Mun rasa mutane biyar a harin gawarwakinsu an gano su ne awanni bayan da aka ci karfin yan ta’addar.amma kuma kusan sojoji 30 suka bace a lokacin da ake tsakiyar gwabzawa,” ya ce.

 Ya ce saura kiris yan ta’addar su kwace sansanin amma daga baya aka samu nasara akansu bayan da aka samu karin sojoji inda aka kashe yan ta’adda masu yawa wasu kuma suka tsere da raunin bindiga.

Wani mamba a kungiyar bijilante  ya fadawa wakilin Jaridar Daily Trust cewa yaga gawarwakin soja biyar ana dauke su a motar ɗaukar marasa lafiya.

“Na gano cewa an dauke gawarwakin zuwa Damaturu ko Maiduguri kuma yan ta’addar sun dauke motocin soja guda biyu an samu galaba akansu ne da taimakon jirgin yaƙi da ya kashe da yawa daga cikinsu,” ya ce.

Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya ta uku, Kanal Kayode Ogunsanya  ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai amma ya musalta cewa an samu asarar rayuka.

You may also like