BokoHaram: Ana Kashe Milyan 15 A Kowacce Rana Wajen Shan Man Jiragen YakiMinistan Yada Labarai, Lai Mohammed ya yi karin haske kan kudaden nan na Sama da Naira Bilyan 360 da gwamnonin jihohi suka bayar da gudunmawa don yaki da Boko Haram inda ya nuna cewa, za a yi amfani da kudaden wajen yaki da barayin Shanu da kuma masu satar mutane.

Ya ci gaba da cewa yakin da ake yi da Boko Haram ba kananan kudade yake lakumewa ba inda ya nuna cewa a kowace rana jiragen yakin da ke sintiri da kuma kai farmaki suna shan mai har na Naira milyan 15 a kowace rana sannan kuma a cikin watanni 11 an kashe Bilyan 20 wajen sayo kayayyakin gyaran jiragen.

You may also like