BOKOHARAM: Harin Kunar Bakin Wake Ya Hallaka Mutum 8 a Maiduguri. 


A yayin da ake jimamin mutuwar wasu mutane biyar da mayakan Boko Haram suka kashe a jiya Talata a wani kauye da ke Maiduguri, a yau Laraba kuma wata mota dauke da mata hudu da direba dauke da abubuwan fashewa ta tarwatsa a kusa da garajin Muna da ke cikin Maiduguri inda mutane takwas suka rasa rayukansu.
Da yake tabbatar da harin, Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Borno, Victor Isuku ya nuna cewa harin ya yi sanadiyyar raunana mutane 15 wadanda a halin yanzu ake duba lafiyarsu a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri. Ya ce motar da abin ya faru da ita kirar Golf ce mai lamba JERE 349 XA mai dauke da kalar Taksi ( RTEAN 7179). Ya ci gaba da cewa direban Taksi din ya dauki dan kunar bakin waken ne a kan hanya ba tare da saninsa ba inda yake kan hanyar zuwa garin Gamboru.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like