Rundunar Sojan Nijeriya ta bayyana cewa ta fara aikin gina titina daga garin Alagarno zuwa cikin Dajin Sambisa saboda dakarunta su samun saukin shiga da kayyakin yaki a yayin da ake kokarin murkushen sauran mayakan Boko Haram da ke cikin dajin.
Kwamandan Rundunar shirin ‘ Zaman Lafiya Dole’, Manio. Janar Lurky Irabor ne ya bayyana haka inda ya kuma nuna cewa sojoji sun samun nasarar ceto mata da yara sama da 1800 daga hannun mayakan Boko Haram din wadanda suka yi garkuwa da su a cikin dajin Sambisa.
Ya kara da cewa sojojin sun kuma cafke mayakan Boko Haram 504 wanda mutum 19 daga cikinsu da kansu suka mika wuya sannan ana ci gaba da yin tambayoyi a kan wasu baki daga kasashen ketare don tantance su a kan ko suna da wata alaka da mayakan Boko Haram din.