BOKOHARAM: Sojoji Sun Samu Nasarar Kashe wasu ‘Yan Boko Haram A Garin Ladin Buta Na Jihar Borno


A wata farauta da dakarun sojojin Nijeroya suka fita a a kauyukan Ladin Buta da Juwano duk a karkashin karamar hukumar Jere a jihar Borno, sun ci kari da ‘yan Boko Haram da misalin karfe sha daya na safiyar yau.
Ana zaton ‘yan Boko Haram din sune suka addabi al’ummar yankin da kashe-kashe da sace-sace.
A yayin artabun an kashe ‘yan Boko Haram guda biyu, yayin da kuma saura suka tsira da raunin harbin bindiga. Sannan kuma an gano bindigu, harsashai da wayoyi a wurin ‘yan ta’addan.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like