BokoHaram Sun Sake Kashe Wani Laftanal Kanal Ma Sojojin Najeriya ‘Yan Boko Haram sun sake kashe wani babban hafsan sojan Nijeriya, kamar yadda majiyarmu ta Premium Times ta rawaito.
Hafsan sojan mai rike da mukamin Liyutanal Kanal, mai suna O. Umusu wanda shine kwamandan  Bataliya ta118 Task Force dake jihar Borno, an kashe shine tare da mai tattata masa bayanai sakamakon fashewar wani abu a lokacin da suke kan artabu da ‘Yan Boko Haram a yammacin jiya Litinin.
Majiya daga rundunar sojojin ta bayyana cewa Kanal din shi da tawagarsa suna kan haryar su ta dawowa daga Maiduguri ne zuwa Baga. Lamarin ya auku ne a tsakanin kauyen Sari da Gudumbali. Kuma an ajiye gawarwakinsu a asibitin sojoji kamar yadda majiyar ta kara da cewa.
Wannan shine Kanal na hudu da aka kashe na sojojin Nijeriya a cikin watanni biyu.

You may also like