BokoHaram sun Sako ‘yan Matan Chibok. 


Kungiyar Boko Haram ta sako 21 daga cikin ‘yan matan Chibok da ta sace a watan Afrilu, 2014, kamar yadda wata majiya mai karfi daga fadar gwamnati ta tabbatarwa da kafar yada labarai ta Sahara Reporters.

Majiyar ta kara da cewa sojoji sun kwashi yaran a jirgi mai saukar ungulu a yankin Banki da ke jihar Borno a safiyar yau Alhamis.

You may also like