Kafin Boko Haram Su Kashe Su Kanal Abu Ali, Saida Suka Sami Bayanai Akan Cewa An Rage Sojoji A Sansanin Sojojin Da Yake Jagoranta, Kamar Yadda Wani Jami’in Soja Ya Bayyana A Tattaunawarsa Da Majiyarmu Ta PREMIUM TIMES
A cikin wata hira ta musamman da jaridar PREMIUM TIMES ta yi da wani jami’in Sojin Nijeriya wanda kuma ya nemi a boye sunansa ya ce kashe sojojin Nijeriya da ake yi a dan kwanakin nan ya samo nasaba ne da irin rashin kayan aiki da sojojin suke fama da shi a filin daga.
Yace tun bayan soke kwangilar taya sojojin Nijeriya yaki da kungiyar Boko Haram da gwamnatin Buhari ta yi aka fara samu babban matsala a filin dagan.
Yace Nijeriya sun sami nasara ne a wancan lokacin ‘watan Febrairu’ na shekara 2015 saboda kayan yaki da sojojin da aka yo haya suka zo da shi.
“Bayan Buhari ya soke kwangilan kuwa suka ta fi da abinsu ga shi yanzu sojojin Nijeriya basu da kayan yakin da zasu fuskanci Boko Harm a dajin Sambisa”.
Ya kara da cewa lallai fa idan za a fadi magana ta gaskiya Sojojin Nijeriya na cikin halin rashin kayan aiki a filin daga.
Bayan haka kuma ya ce irin kashe ofisoshi da sojoji mayakan Nijeriya da Boko Haram sukeyi musamman a ‘yan kwanakin nan ya fara zama abin damuwa da a zo a sake shiri.