Kudin fansar kwanan nan da aka ba wa Boko Haram domin fansar ‘yan Matan Chibok sun yi amfani da su ne domin sayen muggan makamai, kamar yadda majiyar sojoji ta shaidawa jaridar Punch. A cewar majiyar, duk da nokewar da gwamnati ta rika yi a karshe sai da aka ba su kudin fansar.
Rahotanni sun bayyana cewa, Boko Haram sun nemi Dala Miliyan 50 domin sakin ‘yan matan, amma a karshe sun samu kaso hudu daga cikin kudin. Inda aka raba su kaso biyu Naira da kuma kudin kasar Faransa. Sai dai fadar shugaban kasa ta karyata cewa ta bayar da kudi kafin musayar ‘yan Matan.