BokoHaram Ta Kai Sabon Harin Kunar Bakin Wake A Borno



Rahotanni sun tabbatar da cewa a yau Alhamis ne, wani dan kunar bakin wake ya samu nasarar tarwatsa kansa a kauyen Amarwa da ke cikin karamar Hukumar Konduga a jihar Borno inda ya kashe mutane hudu yayin da wasu mutane 13 suka raunana.

Kamfanin Dillancin Labaru na Nijeriya ya ruwaito cewa al’amarin ya auku ne da misalin Karfe biyu na rana bayan da dan kunar bakin waken ya samu sa’ar shiga kauye inda ya ce shi dan kasuwa mai sayar da hatsi wanda daga baya ne ya je inda wasu ‘yan kauyen ke hutawa a gindin bishiya kuma ya tarwatsa Bom din da ke jikinsa.

You may also like