
Asalin hoton, Twittter/@officialABAT
Dan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar APC a zaben 2023, Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin janye tallafin man fetur da zarar ya zama shugaban kasar.
Tinubu ya bayyana haka ne ranar Alhamis da daddare a yayin da yake gudanar da taro da wasu ‘yan kasuwar kasar.
“Dokar man fetur tana nan kuma za mu duba ta a karo na biyu domin sauke nauyin da ke kanmu kuma duk zanga-zangar da za a yi, za mu cire tallafin man fetur,” in ji Tinubu.
Ya kara da cewa: “Za mu dauki matakai masu tsauri, wannan shi ne batun gaskiya. Don haka wajibi ne mu cire tallafin man fetur.”
Ya ce ba zai ci gaba da bayar da tallafin man fetur ba saboda kasashe makwabta irin su Kamaru, Jamhuriyar Nijar, Jamhuriyar Benin ne suke cin moriyar hakan.
Tinubu ya kara da cewa zai sanya kudin da ake biyan tallafin man fetur a fannonin da suka kamata irin su lafiya.
Kazalika ya ce zai cire jerin haraje-haraje da hukumomi suke karba yana ma cewa zai sa a rika karbar haraji daya kan mu’amalar da ta shafi a biya mata haraji.
Bayanai sun nuna cewa gwamnatin Najeriya ta biya N1.9 daga watan Janairu zuwa watan Yulin 2022 kadai, lamarin da wasu ke ganin ba abu ne mai dorewa ba.
Da ma dai shi ma dan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya dade da shan alwashin janye tallafin man fetur idan ya zama shugaban kasa. Ya ce tallafin ba ya yi wa talakawa amfani.
A baya dai, ‘yan kasar sun gudanar da jerin zanga-zanga sakamakon matakan da gwamnatoci suka dauka na janye tallafin man fetur.