Boma-Bomai Biyu Sun Tashi A Garin Mandagali Na Jihar Adamawa Boma bomai guda biyu ne suka tashi a garin Magadali da ke jahar Adamawa a yau Juma’a wanda ya haddasa rasuwar mutane da dama.

An kai harin ne a wata kasuwa a yau, sai dai har yanzu ba a samu cikakkun bayanai akan al’amarin ba.

Garin Magadali dai ya na da nisan kilomita 276 daga Yola, babban birnin jahar Adamawa, kuma ya na kusa da jahar Borno.

 

Garin na daya daga cikin garuruwan da Boko Haram suka kwace a lokacin da suka yi ganiyar su.

Wannan dai shi ne karo na uku da mayakan Boko Haram suka kai hari a garin Magadali. A watan Disambar shekarar da ta gabata ma, wasu mata ‘yan kunar bakin wake sun kai hari a wata tashar mota da ke garin inda suka hallaka mutane 30, guda 16 kuma suka jikkata

You may also like