An bude jami’ar Musulunci ta farko a kasar Spaniya


 

An bude jami’ar kimiyyar Musulunci ta farko a cibiyar raya al’adun Musuluncida ke garin San Sebastian na kasar Spaniya.

Wakiliyar jami’ar Badar Hijra an fara rajistan daliban wannan shekara kuma daliban za su iya samun dukkan kayan karatun a shafukan yanar gizon jami’ar.

Ta ce, bayan shekaru 4 za a fara karatun digiri na 2 da digirgir a jami’ar.

Gwamnan San Sebastian Eneko Goia ya bayyana cewa, wannan wata babbar dama ce da za a san al’adun Addini a garin.

 

You may also like