BUHARI @75: TAKAITACCEN TARIHIN MUHAMMADU BUHARI An haifi shugaban Nigeria muhammadu buhari A ranar 17 ga watan decemba shekara 1942 a cikin garin daura dake jahar katsina arewacin Nigeria

  Shugaban Nigeria muhammadu buhari shine mutun na 23 Akun mahaifin shi malan Adamu sannan ya tashi A hannun mahaifiyar shi mai suna zulaihatu bayan rasuwar mahaifin shi yana dan shekara 4 Aduniya 

Buhari yayi karatun Addini A Gida inda yashiga makarantar primari ta daura da mai,aɗu a sannan yaje katsina model school A shekarar 1953 sai kuma katsina Provincial secondry shool ( Wanda Ake kira da Government college katsina Ayinzu ) daga 1956 zuwa 1961 

Daga nanne buhari yatafi makarantar soja dake garin kaduna Ayinxu haka

Kafin buhari yaxama shugaban Nigeria na farko A 1983 yarike wasu manya manyan mukaman gwamnati wa inda suka hada da gamnan jahar Arewa Maso gabas da ministan man fetar da Albarkatun kasa 

Tundaga nan tauraruwar buhari tafara haskawa Aduniya domin ganin yadda yakeda gaskiya wajan rikon Amana da tsire dukiyar kasa

Ashekarar 1983 ne muhammadu buhari da Abokansa cikin rundunar sojojin kasar sukayima shehu shagari juyin mulki saboda zarkin chanhanci da rashawa da yayyawa tsakanin ma’akatan gwamnatinshi da wasu yan siyasa

buhari yajagoranci Nigeria na tsawan watanni 20 muhimman Abubuwan da buhari yayi Awanchan lokacin sun hada da farfado da tattalin Arzikin Nigeria chanza launin kudaden Nigeria domin rusa marayin gwamnati inganta harkar bankunan Nigeria domin sukara karbuwa Aduniya 

Alokacin muhammadu buhari yayi yinkurin gyara halayyar yan Nigeria inda yajefa wasu manyan yan siyasa gidan kurkuku saboda daidaituwar Nigeria 

Alokacin ne mummadu buhari ya gabatar da shirin yaki da rashin da,a da nufin kyautata halaiyen yan Nigeria saidai muhammadu buhari yasha suka daga bangare daban daban Na duniya Awanchan lokacin 

Saboda kyekkyewar niyar da muhammadu buhari yakeda shi Akan Nigeria ne yasa ibrahim badamasi babangida yamai juyin mulki Ashekarar 1985 

Tunda babangida yama muhammadu buhari juyin mulki bai kara samun wata damar shiga gwamnati ba sai mulkin Abacha lokacin da yakafa huƙumar PTF inda ya dauko muhammadu buhari yabashi shugabancin hukumar A 1994 

PTF hukumace wacce take tara rarar man fetur domin yima kasa Aiki

Tabbas muhammadu buhari yataka rawar gani lokacin da yake rikye da hukumar PTF 

Lokacin da muhammadu buhari yake rikye da hukumar PTF yayi ayyuka kamar haka 

Makarantu

Asibitoci

hanyoyo 

Dadai sauran Abubuwan da yan Nigeria bazasu taba mantawa dasu ba

bayan mutuwar Abacha A 1988 zuwa 1999 ne muhammadu buhari yashiga harkar siyasa gadan gadan 

Muhammadu buhari yafara tsayawa takara A 2003 Akarkashin jam,iyar ANPP inda Allah baibashi nasara ba yakara fituwa A 2007 Acikin jam,iyar ANPP nanma Allah baibashi ba sannan yakafa jam,iyar shi mai suna CPC inda yakara tsayawa takara Acikinta A 2011 nanma Allah baiso yazama shugaban Nigeria ba sai A 2015 

Idan muka dubi halin da Nigeria ke ciki Alokacin mulkin shehu shagari yayi daidai da lokacin da PDP ke mulkin Nigeria tsakanin 1999 zuwa lokacin da muhammadu buhari yadawo mulkin Nigeria karo na biyu 2015 

Lallai Akwai jan Aiki Agun muhammadu buhari dubada yaɗɗa Al,Amuran Nigeria suka lalace lokacin mulkin PDP 

Saidai muna rokon ubangiji Allah yataimaki shugaban Nigeria muhammadu buhari Akan niyarshi ta Alkairi

You may also like