Samuel Oryom, gwamnan jihar Benue ya bayyana cewa shugaban kasa,Muhammad Buhari ba shine ke da alhakin kisan mutanen da ake ba a jihar Benue.
Da yake magana da manema labarai ranar Talata, Ortom ya ce tun gabanin gwamnatin Buhari ake rikicin Fulani da manoma. Zai zama gurguwar fahimta idan aka alakanta Buhari da kisan.
Gwamnan ya ce akwai fulani makiyaya nagari a jihar Benue da suke bin doka.
“Tabbas Buharin zai zo nan yakin neman zabe bazan iya amayar da abin da zai ce ko kuma wanda mutanen jihar Benue za su fada. Amma kamar yadda kuka sani a siyasa babu makiyi ko kuma aboki na din-din,”ya ce.
Gwamnan ya bayyana kungiyar Miyetti a matsayin wacce take taki yaki da al’ummar jihar.