Buhari Bai Samu Damar Halartar Zaman Majalisar Ministoci BaRahotanni daga Fadar Shugaban kasa sun tabbatar da cewa Shugaba Muhammad Buhari bai samu halartar zaman majalisar ministoci da aka saba yi a kowace ranar Laraba wanda wannan shi ne karo na biyu da Shugaban bai halarci zaman ba tun bayan da ya dawo jinya daga waje.

An dai ruwaito cewa a lokacin da Mataimakin Shugaban, Osinbajo da wasu ministoci ke jiran isowar Shugaban, sai ga jami’in kula da Harkokin Fadar Shugaban ya shigo zauren taron inda ya sanar da Mataimakin sakon Shugaban wanda daga nan ne Mataimakin Shugaban ya jagoranci zaman majalisar.

You may also like