Buhari Bai Sanar Damu Kan Tazarcen Sa Ba – APCShugaban jam’iyyar APC na Kasa, Cif John Oyegun ya tabbatar da cewa jam’iyyar ba ta da masaniya game da shirin Shugaba Muhammad Buhari na sake tsayawa takara a zaben 2019.

Haka ma, shugabannin jam’iyyar na jihohi sun nuna cewa Buhari bai sanar da su kan cewa yana son yin tazarce ba. Ana dai ci gaba da yayata rahotannin cewa Buhari ya nada Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi a matsayin Shugaban yakin neman zabensa a 2019.

You may also like