Buhari da Obasanjo sun haɗu a Ethiopia


Shugaban ƙasa Muhammad Buhari da tsohon shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, fuskokinsu sun kasance cikin annashuwa lokacin da suka haɗu   a wajen babban taron kungiyar Tarayyar Afirka AU dake gudana a birnin Addis Ababa na ƙasar Ethiopia.

Hakan na zuwa ne kwanaki biyar bayan da Obasanjo ya rubuta wasika mai ɗauke da zafafan kalamai inda a ciki ya nemi Buhari ya hakura da takara a shekarar 2019.

Sun yi musabaha kana suka tattauna ta tsawon mintuna biyu abin da ya jawo hankalin mutanen dake cikin ɗakin taron.

Hadi Sirika ministan sufurin jiragen sama da kuma Geoffrey Onyeama ministan harkokin waje tare da sauran ƴan tawagar Najeriya a wurin taron sun shiga murmushi ya yin da suke kallon abinda yake faruwa daga nesa.

Daga bisani tsohon shugaban kasa Abdulsalam Abubukar yazo inda suka dauki hoto.

You may also like