Buhari, DANGOTE, Dahiru Bauchi, sun shiga Sahun Mafi Shaharar Musulmi 500 na Duniya. 


 

Buhari, Sultan, Sheik Dahiru Bauchi, Dangote Da Sauran ‘Yan Nijeriya Guda Tara Sun Shiga Cikin Sahun Mutanen Da Suka Fi Shahara A Duniyar Musulunci

*Adadin Yawan Musulman Duniya Sun Kai Bilyan 1.7

‘Yan Nijeriya 13 ne aka shigar da sunayensu cikin jerin mutane 50 da suka fi shahara a duniyar musulunci, ciki har da shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, da Sheikh Ibrahim Saleh na jihar Barno.
Shugaba Buhari ne na 17 a jerin, hakan na nuna ya kara yin sama kenan daga matsayin na 20 da yake a bara, inda mai Alfarma Sarkin Musulmi yake matsayi na 22, daga na 24 da yake a bara.

An yi wa jerin sunayen taken ‘musulmai 500 a duniya da suka fi shahara’ kuma an fitar da shi ne a ranar Alhamis, 6 ga wannan wata (Oktoba), inda ya nuna yawan musulmai a duniya ya kai biliyan daya da miliyan dari bakwai (1.7 billion).

Dauke a cikin jerin sunayen har da na shugaban kungiyar musulmi ta Ansar-Ud-Deen na Najeriya Dakta Abdulrahman Olanrewaju Ahmad, Dr Ibrahim Datti Ahmed, Prince Bola Ajibola, Imam Muhammad Ashafa, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Alhaji Aliko Dangote, Sheikh Yakubu Musa Katsina, Prof Ishaq Olanrewaju Oloyede, Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi II, shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau da Sheikh Ibraheem Zakzaky, sai dai basa cikin jerin mutane 50 na farko.
Rahoton ya ce mutane 500 da aka lissafa sun jagoranci akalar al’ummar musulmi, ta hanya mai kyau ko mara kyau, ya danganta da fahimtar mutane. “idan aka duba jerin mutane 50 na farko, za’a gane cewa dukkanin su kodai malamai ne ko shugabannin kasashe ne wadanda ba za’a taba banzatar da su ba, musamman ma shugabannin kasashe wanda suke nada malamai.”

Ga sunayen jerin mutane 50 na farko:

HE Professor Dr Sheikh Ahmad Muhammad Al-Tayyeb (Egypt)
HM King Abdullah II ibn Al-Hussein (Jordan)
HM King Salman bin Abdul-Aziz Al-Saud (Saudi Arabia)
HE Grand Ayatollah Hajj Sayyid Ali Khamenei (Iran)
HM King Mohammed VI (Morocco)
HE Justice Sheikh Muhammad Taqi Usmani (Pakistan)
HE Grand Ayatollah Sayyid Ali Hussein Sistani (Iraq)
HE Recep Tayyip Erdogan (Turkey)
HE Sheikh Abdullah Bin Bayyah (Mauritania)
Amir Hajji Muhammad Abd Al Wahhab (Pakistan)
HM Sultan Qaboos bin Sa’id Aal Sa’id (Oman)
HH General Sheikh Mohammed bin Zayed Al-Nahyan (United Arab Emirates)
HE President Joko Widodo (Indonesia)
Prince Muhammad bin Naif bin Abdul-Aziz Al-Saud and Prince Muhammad bin Salman bin Abdul-Aziz Al-Saud (Saudi Arabia)
HE Sheikh Abdul-Aziz ibn Abdullah Aal Al-Sheikh (Saudi Arabia)
Sheikh Ahmad Tijani bin Ali Cisse (Senegal)
Shugaba Muhammadu Buhari (Nigeria)
HE Sheikh Dr Ali Goma’a (Egypt)
Sheikh Salman Al-Ouda (Saudi Arabia)
Dr KH Said Aqil Siradj (Indonesia)
HE President Abdel Fattah Saeed Al-Sisi (Egypt)
Amirul Mu’minin Sultan Muhammadu Sa’adu Abubakar III (Nigeria)
Mufti Muhammad Akhtar Raza Khan Qaadiri Al-Azhari (India)
HE Mohammad bin Mohammad Al-Mansour (Yemen)
Habib Umar bin Hafiz (Yemen)
HE Sheikha Munira Qubeysi (Syria)
Rached Ghannouchi (Tunisia)
HH Emir Sheikh Tamim bin Hamad (Qatar)
Dr Amr Khaled (Egypt)

President Mahmoud Abbas (Palestinian Territories)
Sheikh Dr Yusuf Al Qaradawi (Qatar)
HM Queen Rania Al-Abdullah (Jordan)
Sheikh Hamza Yusuf Hanson (United States of America)

Moez Masoud (Egypt)
Seyyed Hasan Nasrallah (Lebanon)
Habib ‘Ali Zain Al Abideen Al-Jifri (United Arab Emirates)
HRH Shah Karim Al-Hussayni (France)
HE Sheikh Ibrahim Salih (Nigeria) Maulana Mahmood Madani (India)
Professor Dr Seyyed Hossein Nasr (United States of America)
Professor Dr M Din Syamsuddin (Indonesia)

Amir Sheikh Mohammed bin Rashid Al-Maktoum (United Arab Emirates)
Sheikh Usama al-Sayyid Al-Azhari (Egypt)
Khaled Mashal (Palestinian Territories)
Habib Luthfi bin Yahya (Indonesia) Abdul-
Malik Al-Houthi (Yemen) Mustafa Hosny (Egypt)
Hodjaefendi Fethullah Gülen (Turkey)
Sheikh Mahmud Effendi (Turkey)
50. Dr Aref Ali Nayed

You may also like