Buhari ga yan Najeriya :Ku karbi katun zaben ku domin ku zabi wanda ranku yake so


Shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi kira ga yan Najeriya da su fito su karbi katin, zabensu na din-din domin su zabi yan takarar da suke so a zaben shekarar 2019.

Buhari wanda yake neman a sake zaben sa a karo na biyu ya bayyana haka lokacin da yake karbar bakuncin wasu alkalai a fadar shugaban kasa dake Abuja ranar Talata da daddare.

Ya alakanta da nasarar da ya samu a zaben shekarar 2015 ga cigaban fasaha, ya shawarci gwamnoni da kada su yi kasa a gwiwa wajen ilimantar da masu kada kuri’a.

Shugaban Buhari ya bayyana nasarar da ya samu a zaben shekarar 2015 da yin amfani da na’urar tantance rijistar masu kada kuri’a inda ya ce kafin fara amfani da na’urar ana rubuta sakamakon zabe ne rumfunan zabe.

Da yake nasa jawabin a madadin alkalan tsohon babban jojin kasarnan, Alfa Belgore ,ya yabawa shugaban kasar kan yadda yake nuna kishin kasa inda ya shawarce shi da ya jawo mutanen kirki kusa da shi.

Belgore ya kuma bayyana cewa matsalar tattalin arziki da ake fama da ba kasarnan ka wai ta shafa ba matsala ce dake damun kasashe da dama.

“Naga ya zamo mini dole na gayyace ku saboda ban cika ganinku b

You may also like