Buhari Na Gudanar Da Gwamnatin Mutum Daya – Ghali Umar Na’abba


Tsohon kakakin majalisar wakilan Nijeriya, Ghali Umar Na’Abba, ya bayyana takaici da kuma dana sanin barin jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC a shekarar zabe ta 2015.

Na’Abba ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da jaridar Vanguard inda ya zargi shugaba Muhammadu Buhari da gudanar da gwamnatin mutum guda.

Tsohon kakakin ya ce shi fa bai cimma burin da ya ke so ya cimma ba na dalilin barinsa PDP zuwa APC, sai ma nadama da ya yi na yin hakan.

A cewar Na’Abba, ” Jam’iyyar APC ce ta kawo shugaba Muhammadu Buhari kan karagar mulki, amma sam Buharin baya tafiya da jam’iyyar da tsare-tsarenta. Hasali ma gwamnatin na tafiya ne akan tsarin Buhari a matsayinsa na Buhari shi kadai tilo.

“Shi yasa ma da yawa daga cikin mutanen da suke tare da Buhari shekaru 12 da suka wuce suka kama gabansu ssaboda kasa fahimtar yadda ake gudanar da gwamnati.

“A shekara uku da na kwashe a APC, jam’iyyar ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki sau 4 kacal. Na farko a n yi shi a watan Fabrairun 2016, sai kuma aka sake yin wani bayan watanni 16 a watan Oktoba zuwa Nuwanban 2017.

Ba a gayyaceni sauran tararrukan ba saboda a wata hira da gabatar na bayyana cewa ba zan goyi bayan sake tsayawar Buhari ba a shekarar 2019.

“A duk lokacin da jam’iyya ta zama ba ta iya karbar suka ko ra’ayin ‘ya’yanta ko shakka babu za a samu matsala a yanayin yadda a ke gudanar da dimokuradiyya a tsarinta.

“APC jam’iyya ce ta hadakar jam’iyyu da ra’ayoyi da suka hadu da nufin su ture mulkin PDP kuma suka yi nasara da izinin Allah.

“Amma a maimakon shugaba Buhari ya yi la’akari da yanayin jam’iyyar ta kasancewanta na kazo-na-zo ta yadda zai samar da hadin-kai da jituwa tsakanin ‘yan jam’iyya, sai ya buge da gudanar da jam’iyyar shi kadai ba tare da tsoma ‘yan jam’iyya ko majalisar tarayya ba.

“Yanzu ga sakamakon nan ya bayyana a zabukan shugabannin jam’iyya na jihohi da aka gudanar, inda aka samu rarrabuwar kawuna a kusa dukkan jihohin kasar, baya ga barazana da ‘yan sabuwar PDP da suka narke a APC suke yi na bari jam’iyyar.

“Wadanda kawai a ke yi da su a gwamnatin Buhari sune wadanda suka fito daga jam’iyyar ACN da wasu tsirari daga CPC.

“Ana ta tafiyar da jam’iyyar kamar ba jam’iyya ba saboda babu fahimta tsakanin jam’iyyar da shugaban kasa haka kuma abun ya ke a jihohi.

“Jam’iyyar na motsawa ne kadai in har shugaban kasa ko gwamnoni a matakin jijhohi na son yin amfani da jam’iyyar. A wannan lokaci ne fa za ka ga sun taka doron jam’iyyar don yin yadda suke so.

“Da wannan dalili ne na ke cewa a gaskiyar magana bani da wata hujja da zan nuna cewa APC ta fi min PDP,” inji Ghali Na’Abba.

You may also like