Buhari Na Shirin Jefa Najeriya A Cikin Yaki – Dattawa Kiristocin Najeriya Inuwar Dattawan Kiristoci Ta Najeriya (NCEF) ta zargi gwamnatin Buhari da laifin rikicin kabilanci da kuma tunzurin rikicewar kasar nan. A cewar su da gangan gwamnatin ta tatsile kundin tsarin mulkin kasa da kuma yarjejeniyar zaman tare. 

Kungiyar wacce ta hada manyan kusoshin janar na soja, ciki har da tsohon ministan tsaro TY Danjuma, ya soki yadda aka yi wa rikicin Fulani/makiyaya rikon Sakainar-kashi, kana kuma ya yi gargadin cewa, masu tsatstsauran ra’ayin addini na kada gangar Jihadi. 

A cewar su, wannan gwamnati na yunkurin hankada kasar zuwa kwazazzabon zubar da jini. Daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada Mr. Danjuma, Solomon Asemota, Joshua Dogonyaro da Zamani Lekwot.

You may also like