Buhari na shirin yin karin nade-naden mukamai


Shugaban kasa Muhammad Buhari, nan ba dadewa zai yi nade-naden mukamai ciki har da karin wasu ministoci tare da shugabannin hukumomin gudanarwa na ma’aikatu daban daban-daban.kamar yadda jam’iyarsa ta APC ta bukaci yayi haka.

Buhari ya bada haske kan shirin nasa na yin nade-naden mukaman a cikin jawabinsa da yayiwa kwamitin zartarwar jam’iyar APC a Abuja.

A yanzu haka dai akwai ministoci 36 a gwamnatin Buhari kuma 14 daga ciki suka kasance kananun ministoci inda shugaban da kansa yake jagorantar ma’aikatar man fetur.

Shugaban kasar ya ce yadade yana aiki da ministocin kadan a kokarin da yake na tsuke bakin aljihun gwamnati amma kuma nan ba dadewa ba hakan zai zama tarihi.

Ya ce za a sake buda majalisar zartarwa ta tarayya daga yadda take a tsuke yanzu domin shigo da magoya baya  da kuma sababbin jini dake cike da basira da hazaka.

Sai shugaba Buhari bai nuna alamar zai gudanar da tankade da rai raya  ba ga majalisar zartarwar tasa.

“Shekarar da ta wuce na ce zan sake nada yan kwamitin gudanarwar hukumomin gwamnati dole ne nayi da sanin rashin yin haka saboda wasu dalilai masu yawa,”yace 

” A wani bangaren ina sane da cewa magoya baya sun kagu sosai a fadi wadannan mukamai da za nada, da izinin Allah za a fadi wadannan mukamai nan ba dadewa ba, musamman ma yanzu da tattalin arzikin mu yake sake inganta zamu samu kudin da za mu iya kula dasu.”


Like it? Share with your friends!

0

You may also like