Buhari ya aika da sunaye biyu majalisa da za a naɗa ministoci.


muhammadu-buhari2

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya tura da sunayen mutane biyu zuwa majalisar Dattijai domin tantance su da kuma tabbatar dasu a matsayin ministoci a majalisar zartarwa ta tarayya.

Takardar data isa majalisar dattijai jiya da yamma na dauke da sunan mutum biyu daga jihar Gombe da kuma Kogi.

Wanda aka zaɓa daga kogi zai maye gurbin tsohon karamin ministan kwadago da nargatar aiki James Ocholi, wanda yarasu sakamakon haɗarin mota akan hanyar Kaduna zuwa Abuja a watan maris na shekarar data gabata.

Yayin da wanda aka zaɓa daga jihar Gombe zai maye gurbin Amina Muhammad tsohuwar ministar muhalli wace a yanzu take mataimakiyar shugaban majalisar dinkin duniya.

Buhari ya aika da sunayen ne loakcin da ake samun takun saƙa tsakanin bangaren zartarwa da kuma majalisar ta dattijai kan batun tabbatar da shugabancin shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu.

 

You may also like