Buhari Ya Ankarar Da ‘Yan Siyasa Kan Tsaftace Kalaman Yakin Neman Zabe
Yanzu haka dai ‘yan Najeriya na ci gaba da fashin baki da tofa albarkacin baki kan yadda ya kamata ‘yan siyasa da magoya bayansu su tunkari tallan ‘yan takara, musamman a kafafen yada labarai.

Ranar Larabar da ta gabata ita ce ranar da a hukumance aka baiwa jam’iyyun siyasa da ‘yan takara su fara gangamin neman kuri’ar ‘yan Najeriya, musamman a matakan shugaban kasa da ‘yan majalisar dokoki na kasa, kamar yadda yake kunshe a jadawalin hukumar zabe ta INEC.

Sai dai a yayin da ya sha alwashin gudanar da sahihin zabe a shekara ta 2023, shugaba Muhammadu Buhari ya ankarar da ‘yan siyasa su guji kalamai marasa tsafta a yayin tarukan neman kuri’ar ‘yan kasa da kuma kafofin labarai.

To amma Anas Abba Dala wani dan Jam’iyyar APC a Kano, ya ce jami’an gwamnatin da shugabannin jam’iyyar su ta APCn ne za su fara nuna misali, yana mai cewa, zai yi wahala a ce mai rike da madafun iko ya ci zarafin dan hamayya a yayin neman kuri’a kuma yayi zaton shi ma a kyale shi.

A hannu guda kuma kalaman da kan fito daga bakunan magoya baya masu shiga kafofin labaru su tallata ‘yan takara na tasiri wajen fayyace sahihancin gudanar da yakin neman zabe cikin tsafta.

Abdullahi Maikano Zara ya ce akwai bukatar masu tallata ‘yan takara su kiyaye harshe, muddin ana bukatar gudanar da hada-hadar zabe cikin lumana.

Yakin neman zabe ta kafofin sada zumunta da ake kira ‘social media’ na cikin babban kalubalen ga sha’anin zaben Najeriya, la’akari da yadda ake amfani da kafofin wajen yada labaru karya.

Sai dai Alhaji Jafar Sani Bello, mutumin da ya nemi tsayawa takarar gwamnan Kano a jam’iyyar PDP, ya ce dole ne a wayar da kan masu amfani da kafar sadarwa ta sada zumunta, kuma a fadakar da mutane game da muhimmancin neman hakki ta hanyar tafiya kotu kai tsaye a duk lokacin da wani yayi amfani da kafar facebook da dangoginta ya ci zarafin wani.

A makon da ya gabata ne dai hukumar kula da kafofin watsa labarai na radio da talabijin NBC ta gudanar da taron bita a jihar Kano, game da dokoki da ka’idojin gudanar da shirye-shiryen siyasa da tallan ‘yan takara da kuma jam’iyyunsu.

You may also like