Buhari ya bada umarnin binciken wata bakuwar cuta da ta bulla a jihar Jigawa


Shugaban kasa Muhammad Buhari ya umarci ministan lafiya Isaac Adewole da ya binciki rahoton wata bakuwar cuta da ta jawo mutuwar yara da yawa a jihar Jigawa.

Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da yafitar a ranar Laraba.

Ya ce shugaban kasar ya umarci ministan, da ya dau duk wani mataki da ya dace domin shawo kan cutar da ta barke a kauyen Gidan Dugus dake gundumar Wangara a ƙaramar Hukumar Dutse ta jihar.

Shehu ya ce Buhari, ya kira gwamna Badaru ta wayar tarho domin sanin cikakken abinda yake faruwa. Kana ya jajantawa gwamnan da kuma iyayen da suka rasa ƴaƴansu.

Ya ce shugaban kasar ya tabbatarwa da gwamnan cewa gwamnatin tarayya za ta bada dukkanin gudunmawar da ta dace domin hana cutar bazuwa.

You may also like