Buhari Ya Bar ‘Yan Siyasa Na Juya Shi – Abdulmuminu Jibrin


 

 

 

Dan majalisar wakilan nan da aka dakatar bisa fallasa badakalar aringizon Kasafin kudi, Abdulmumini Jibrin ya nuna rashin jin dadin sa game da yadda ya ce shugaban kasa Buhari ya bari wasu manyan ‘yan siyasa a kasar suna juya shi.

Ya fadi haka ne a wasu sakonni da ya wallafa a shafin sa na Twitter inda a daya daga cikinsu ya bayyana cewa shugaban kasar da ba zai iya gane hanyar da zai bullowa makircin ‘yan siyasa ba, to abun da ya kamace shi shi ne ya yi murabus.

Ya zargi Buhari da barin wasu ‘yan tsiraru da basu yadda da amincinsa ba sun na juya shi yadda suka so.

Ya fada cewa shugaban zai dawo ga wadannan sakonni da ya wallafa watanni 18 masu zuwa.

Ya kuma ce shugaban kasar ya juya bayan sa ga wasu batutuwa masu muhimmanci a kasar nan saboda ya na yunkurin dadadawa wadannan ‘yan siyasa.

Toh duk da dai jibrin bai fadi wadanda ya ke nufi ba a sakonnin na sa, ana hasashen cewa sakonnin na sa na da alaka da cikar shekaru 49 da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya yi a kwanan nan inda shugaban kasa Buhari ya yi masa murna ya kuma yaba da gudummawar da yake bayarwa wajen ciyar da kasa gaba.

You may also like