Buhari ya bawa yan majalisun tarayya hakuri kan sabanin da suka samu da jami’an tsaron fadar Aso Rock


Shugaban kasa Muhammad Buhari, ya bawa mambobin majalisun tarayya hakuri kan sabanin da yafaru tsakaninsu da jami’an tsaro dake fadar shugaban kasa.

Karkashin jagorancin shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da Yakubu Dogara yan majalisar sun je fadar Aso Rock domin ganawa da shugaban kasa.

Ganawar tasu na da nasaba da batun kasafin kudin shekarar 2018.

Amma kuma sun bar fadar shugaban kasar cikin fushi bayan da jami’an tsaro suka dage kan cewa sai sun tantance su kafin abarsu su shiga.

Daga bisani shugaba Buhari ya nemi yan majalisar, amma da yawa daga cikinsu  sun riga sun bar gidan shugaban majalisar dattawa inda suka taru bayan abin da ya faru tsakaninsu da jami’an tsaron.

Saraki da Dogara sun dawo fadar shugaban kasar inda aka shirya musu liyafar cin abincin dare da ta samu halartar shugaban kasa Muhammad Buhari, mataimakinsa Yemi Osinbajo, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa,Abba Kyari da kuma Sulaiman Kawu da Ita Enang, masu taimakawa shugaban kasar kan harkokin majalisun tarayya.

Saraki ya tabbatarwa da manema labarai cewa an warware matsalar.

You may also like