Buhari Ya Bayar Da Umarni A Binciki Abba Kyari Kan Zargin Karbar Cin Hanci Daga MTN


abba-kyari

 

Shugaban Ma’aikatan fadar shugaba Muhammadu Buhari, Alhaji Abba Kyari na fuskantar bincike daga wata tawagar bincike ta musamman ta hukumar ‘yan sanda ta kasa bisa zargin cin hanci da rashawa

Binciken na da alaka da zargin da ake yi wa Abba Kyari na karbar cin hancin Naira miliyan 500 daga hannun kamfanin sadarwa na MTN mallakar kasar Afirka ta Kudu don taimaka wa kamfanin hana gwamnatin tarayya ci gaba da bibiyar tarar dala biliyan 5 aka ci MTN din sakamakon rashin bin dokokin Hukumar Sadarwa ta kasaAbbaBuhari.JPG

In ba a manta ba, jaridar Sahara reporters ta ranar 20 ga watan Satumba, 2016, ta rawaito cewa ragin tarar da aka ci MTN daga dala biliyan 5 (Naira tiriliyan 1.9) zuwa Naira biliyan 300 kacal, ya biyo bayan tuntubar Abba Kyari da Hukumomin kamfanin MTN suka yi suka yi, tare da bashi cin hancin naira miliyan 500 don ya yi amfani da kusancinsa da shugaban kasa ya sa a rage yawan tarar daga dala biliyan 5 zuwa wani adadi kasa da haka
Majiyarmu ta Vanguard ta bayyana cewa, shugaba Buhari ya damu da wannan zargi kwarai inda har ya umarci Sifeton ‘yan sanda ta kasa, Ibrahim Idris da ya gabatar da bincike akan zargi sannan ya mika sakamako binciken ga fadar shugaban kasa

You may also like