Buhari ya Bayyana Cikakken Dalilin Daya Hanashi Halartar Taron Tattalin Arzikin Jihohin  Igbo



Shugaba Muhammad Buhari ya fayyace dalilin da ya sa bai halarci taron tattalin arziki da Harkokin Tsaro na jihohin Kudu maso Gabas ba wanda aka yi a Enugu inda ya nuna cewa ya dauki matakin ne don gudun kada ya kawo wata cikas ga shirye shiryen bukukuwan Kirismeti da aka fara a yankin.
Kakakin Shugaban kasar, Garba Shehu ya ce wasu daga cikin Dattawan. Igbo ne suka ba Shugaban wannan shawara wanda kuma ya tuntubi masu shirya taron kan dage taron zuwa wani lokaci amma kuma suka nace wajen ci gaba da taron wanda ya samu halarci tsohon Shugaban kasa, Cif Obasonjo.
Ana dai zargi Buhari da yin watsi da yankin na Igbo wanda a jawabin da ya gabatar a wurin taron Cif Obasonjo ya nemi al’ummar Igbo kan su fita harkar gwamnatin. Buhari su mayar da hankalin wajen gina yankinsu saboda a cewarsa suna da duk wata kwarewa na cimma wannan buri.

You may also like