Shugaban kasa Muhammad Buhari a ranar juma’a ya bayyana dalilin da yasa ya gana da mataimakinsa Yemi Osinbajo lokacin da yake jiya a birnin London.
Shugaban kasar yace ya kyale mataimakin nasa ya gana dashi ne saboda ya gode masa kan shugabanci nagari da yake gudanarwa lokacin da yake jinyar.
” Shi ( Osinbajo ) yayi amfani da damar karancin shekaru da yake dasu wajen kasancewa a ko ina,”yace.
” Nagode Allah da ya bani da damar lura da irin aikin da yake cikin sa’o’i 24 ta hanyar kafafen yada labarai na taya shi murna na kuma bashi damar yazo ya ganni domin nagode mishi da kaina kan irin namijin kokarin da yayi.”
Shugaban kasar ya bayyana haka,lokacin da yake karbar tawagar gwamnonin jihohi da suka kai masa ziyara a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Shugaban kasar ya kuma yaba da nasarar da kasarnan ta samu a bangaren aikin noma cikin shekaru biyun da suka gabata.
Ya kuma nuna jin dadinsa kan yarda yan Najeriya suka rungumi harkar noma.