Buhari ya Bayyana Yaddw Gwamnatin Sa Zata Kashe Ribar Kasuwar Danyen Man Fetur


Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Najeriya za ta kashe kudaden shigar da za ta kara samu sakamakon tashin farashin danyen man fetur a fannin inganta rayuwar jama’a da ci gaban kasa.

Buhari ya yi wannan jawabin ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kamfanin Eni, a karkashin jagorancin Antonio Vella, wanda shi ne babban jami’in kula da hako mai na kamfanin.

Shugaban Kasa ya ce ribar da za a rika samu daga sama, wadda yanzu ta wuce yadda aka yi tsammanin samu, tunda farashin danyen mai ya tashi a kasuwar duniya, ‘‘za a kashe kudaden ne wayen ayyukan raya kasa wadanda kowa da kowa a kasar nan za su amfana.”

Buhari ya ce za a yi ayyukan titina, layin dogo, inganta hasken lantarki da sauran ayyukan da daukacin jama’a za su dade su na cin moriya a cikin kasar nan.

Buhari ya yaba da irin yadda kamfanin Eni ke narka dimbin jarin sa wajen harkar danyen mai a kasar nan, ciki har da farfado da matatar mai ta Fatakwal da kuma gina wata sabuwa.

Shugaban sai ya nuna takaicin yadda a farkon zaman sa shugaban kasa da farko yadda matatun mai na Warri da Fatakwal ke aiki, amma a yanzu a hawan sa mulki karo na biyu, ta taras da sun zama abin takaici.

Jagoran kamfanin Eni, Antonio Vella, ya bayyana wa Shugaba Buhari cewa sun gabatar wa kamfanin NNPC wani daftari na yadda za su gyara matatar mai ta Fatakwal, sanna kuma su na kan yin bincike da nazarin yadda za su kafa wata matatar da za ta rika tace gangar danyen mai 150,000 a kowace rana.

You may also like