Buhari Ya Bukaci Al’ummar Najeriya Su Tabbatar An Yi Zabe Nagari Badi
Wannan na dauke ne a sakon tayin murnar zagayowar bikin Kirsimeti wanda shugaban kasar ya isar ta bakin kakakinsa Malam Garba Shehu.

Ya ce shugaba Buhari yana fatan cewa, “mabiya addinin Kirista da dukkan al’ummomin Najeriya za su yi kokari su tabbatar da zaman lafiya, su tabbatar cewa an yi zabe cikin gaskiya da kaunar juna, da kuma tabbatar an zabi wanda ake ganin zai gina akan kyawawan ayyukan da gwamnatinsa take yi.”

Malam Garba Shehu ya kara da jaddada dagewar shugaba Buhari wajen kare al’ummomin Najeriya da dukiyoyinsu, tare da cewa gwamnatin tarayya na kara himma don kawo karshen duk ayyukan da ke haifar da hargitsi a fadin kasar.

Shi kuwa limamin cocin St. Andrew’s Basilica da ke Inugu, Venerable Rex Ufomadu ya yi tsokaci kan shagulgulan Kirsimeti da Kiristoci ke yi.

Ya ce, “mutane da dama suna shagali yau ba tare da sanin ainihin dalilin shagalin ba. Sakonmu ga Kiristoci yau shine kada su manta cewa Kristi shine dalilin murnar da ake yi saboda ya zo ne a lokacin da dan adam ya lalata dangantakar da ke tsakaninsa da Ubangiji, kuma shi ya sa Ubangiji ya turo shi a matsayin sulhu.”

Venerable Ufomba dai ya karkare da yin kira ga Kiristoci da su isar da kauna ga Musulmi da sauran jama’a yayin da suke shagulgulan Kirsimeti na wannan shekarar.

Domin Karin bayani saurai rahota cikin sauti:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like