Buhari Ya Dakatar Da Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Lawal Da Shugaban Hukumar Tsaron Ƙasa Ta NIA


babachir

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Sakataren gwamnatin tarayya Babachir David Lawal da Kuma shugaban hukumar tsaro ta ƙasa NIA,  Ayo Oke har sai an kammala bincike.

Wannan na ɗauke a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa Femi Adesina ya fitar a yau Laraba.

Koda a watan Disambar shekarar da ta gabata  sai da Majalisar dattijai ta nemi Babachir da yayi murabus, bayan da kwamitin majalisar kan harkokin jin ƙai a yankin arewa maso gabas ya same shi da laifin cin hanci da rashawa.

Jama’a da dama sun koka kan yadda shugaban ƙasa ya  gaza ɗaukan mataki kan rahoto na majalisar.

“Shugaban ƙasa Muhammadu Buhar yabada umarnin bincike akan zarge –zargen karya dokoki da akewa Sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal wajen bada kwangila ƙarƙashin shirin shugaban ƙasa na tallafawa mutanen arewa maso gabas da ake kira ‘Presidential Initiative on the North-east( PINE)’ a turance.” Adesina Yace

“ Shugaban ƙasa ya dakatar da sakataren gwamnatin tarayya har sai an kammala bincike”

Buhari ya kuma bada umarnin da ayi bincike kan kudin da hukumar EFCC ta gano a Legas a dogon ginin da ake kira Osborne Tower.

“ A wani abu mai kama da haka shugaban ƙasa ya bada umarnin ayi cikakken bincike, kan maƙudan kuɗaɗen ƙasashen waje da hukumar yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ta’annati EFCC,  ta gano a wani gida dake ginin Osborne Tower a Ikoyin jihar Legas, wanda hukumar tsaron ƙasa ta NIA tace nata ne”sanarwar tace

“Binciken zai nemi ƙarin bayani kan yadda hukumar ta NIA ta mallaki waɗannan maƙudan kuɗaɗe, tayaya ta mallaka, kuma waye yabata,sannan a gano ko an saɓawa doka da kuma tsarin tsaro wajen ajiyewa da yin amfani da kuɗin”

“Shugaban ƙasa yabada umarnin dakatar da Daraka Janal na hukumar ta NIA, Ambasada Ayo Oke, har sai an kammala bincike”

“ An kafa kwamitin mutane 14 wanda ya haɗa da minisatan shari’a, da mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro yayin da mataimakin shugaban ƙasa zai jagoranci kwamitin  da zai gudanar da binciken kan dukkanin zarge -zargen biyu”

“Kwamitin zai miƙawa shugaban ƙasa rahotonsa cikin makonni biyu”

“Babban Sakataren da yafi kowa daɗewa a ofishin sakataren gwamnatin tarayya da kuma, da kuma jami’i mafi girman muƙami a hukumar NIA su zasu cigaba da riƙon muƙaman mutanen da aka dakatar”

You may also like