Buhari ya damu da goyon bayan da ISIS ke bawa Boko Haram


Shugaban kasa Muhammad Buhari a ranar Alhamis ya ce ya kadu bayan da ya fahimci alakar dake tsakanin kungiyar Boko Haram da kuma ISIL.

A cewar,Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasar, Buhari ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da Recep Tayyib Erdogan, shugaban kasar Turkiya bayan da suka gama ganawa a Ankara babban birnin kasar.

Shugaban na Najeriya ya ce ya yi farin ciki da ganin yadda gwamnatinsa ta samu nasarar shawo kan rikicin Boko Haram.

“Mun yi mamaki matuka da kuma damuwa kan ikirarin kungiyar Boko Haram na irin abin da suke samu daga ISIS,” yace.

” Mun san cewa zamu iya shawo kan matsalar, kuma mun nuna cewa zamu iya.

” Mun yi farin ciki da kasancewar Turkiya a wani matsayi da za ta iya taimaka mana dama ta dade tana taimakawa bangaren kiwon lafiyar mu da kuma ilimi.”

Shugabannin biyu sun kuma amince su kara karfafa dangantaka tsakanin hukumomin tsaron kasashen biyu domin yaki da ta’addanci.

You may also like