Buhari Ya Dau Alwashin Kawo Qarshen Shigo Da Abinci Daga Waje Kafin 2019Shugaban Kasa, Muhammad Buhari ya yi alwashin ganin cewa Nijeriya ta wadatu da abinci ta yadda za ta daina dogaro daga kayayyakin abinci da ake shigowa da su daga kasashen waje.
A wani mataki na cimma wannan manufa, gwamnatin tarayya da kulla yarjejeniyar da gwamnatin kasar Morocco don samar da takin zamani tan milyan daya a shekara mai zuwa don ganin an wadatar da manoma da takin a daminar badi.

You may also like