Buhari Ya Dora Laifin Hatsarin Yusuf A Wuyan Mukarraban TsaroShugaban kasa Muhammad Buhari ya Dora laifin hatsarin da Dan shi Yusuf yayi a wuyan mukarraban tsaro masu kula da Yusuf din.

Muhammad Buhari ya kalubakanci masu tsare Yusuf din da cewa mai yasa suka bar shi ya fita da misalin karfe takwas 8:00 na dare bare har yayi tseren Mashin.

Rahotanni sun bayyana cewar Halin da Shugaba Buhari ya tarar da Dan nashi Yusuf din ya tayar mishi da hankali sosai.

A Daren ranar da abun ya faru Buhari ya ziyarci Asibitin da aka kwantar da Yusuf din maganar gaskiya Ran Buhari ya dugunzuma sosai kuma irin maganar daya gayawa mukarraban tsaron Yusuf din a dukkan alamu rai zai baci.

Jaridar Dimokaradiyya ta ruwaito cewar mahaifiyar Yusuf Aisha da Ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau da Alhaji Mohammed Bello da matar kakakin majalisar Dattijai Toyin Saraki kusan raba dare suka yi a Asibitin tsaye a kan Yusuf din.

You may also like