Kungiyar kamfe din tazarcen shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ce ‘yan Nijeriya su dena tsorata a kan lafiyar shugaban kasar, domin yana cikin koshin lafiya, har ma ya fi da yawan mazajen Nijeriya kwari.
Mataimakin daraktan kungiyar, Arch Waziri Bulama ne ya bayyana hakan yayin da yake tattaunawa da ‘yan jaridu a Abuja.
Bulama ya ce: “Ina ganin yadda Shugaban kasa yake kai-kawo a cikin wannan kamfe din ya nuna cewar ya fi da yawan mazajen kasar nan kwari. Wannan ne mutumin da a shekarunsa yake kai-kawo daga birni zuwa birni, sannan akalla yake zuwa birane biyu a kowacce ranar mako domin kaddamar da ayyuka, haduwa da shuwagabannin gargajiya da masu ruwa da tsaki, sannan kuma ya dawo domin ya fuskanci wasu ayyukan kasa da kuma wasu kungiyoyin a fadarsa ta Aso Rock.
Bayan nan kuma da safiyar washegarin ranar ya kuma shillawa wani garin ba tare da nuna alamar damuwa ko rauni ba. Shugaban kasa Buhari yana da lafiya da matukar kwarin da zai gabatar da ayyukansa, sannan kuma abun alfahari, yana bayar da irin shugabanci da lokacinsa da muke bukata a wannan kamfe din.”