Shugaban kasa Muhammad Buhari a yau Litinin ya karbi bakuncin shugaban kasar Cote D’Ivoire, Alassane Quattara a fadar shugaban kasa ta Aso Rock dake Abuja.
Quattara wanda ya isa fadar shugaban kasa da misalin ƙarfe 12:15 na rana an gabatar dashi ga wasu ministoci, masu taimakawa shugaban kasa, kafin su fara ganawar tasu da shugaban kasa.
Wannan ne dai karo na farko a hukumance da shugabannin biyu suke haduwa tun bayan da aka rantsar Buhari a matsayin shugaban ƙasa a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2015.
Ziyara ta karshe da Quattara ya kai wa Buhari ita ce a ranar 20 ga watan Afirilun shekarar 2015 kafin a rantsar dashi a matsayin shugaban kasa.