Buhari ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka a fadar Aso Rock


Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson  a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Ana san ran Tillerson  tare da ministan harkokin waje Geofrey Onyeama za su gana da manema labarai bayan ganawarsa da shugaban kasa Buhari.

An fara ganawar ne bayan da Buhari ya dawo daga ziyarar da ya kai jihar Benue.

Shugaban kasar yaje ne domin ya yi wa mutanen jihar ta’aziya bayan da wasu mutane da ake zargin fulani makiyaya ne suka kashe mutane  sama da 70 a farkon watan Janairun shekarar da muke ciki.

Sakataren harkokin wajen Amurkar zai bar Abuja a yau bayan ya gana da manema labarai.

Wannan ce dai ziyararsa ta farko a yankin Afirka tun bayan da ya kama aiki.

Kafin isowarsa Najeriya Tillerson ya ziyarci kasar Ethiopia, Kenya, Djibouti.

 

You may also like