A yanzu haka shugaban kasa Muhammad Buhari na can na wata ganawa da shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki da kuma kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara.
Ganawar na gudana ne a cikin fadar shugaban kasa ta Aso Rock.
Ganawar ta shugaba Buhari da Saraki da kuma Dogara na zuwa dai-dai lokacin da batun cire wasu kudade daga asusun rarar mai domin sayo jiragen yaki daga kasar Amurka ya jawo ce-ce kuce har ta kai wasu yan majalisa na kira da a tsige shugaban kasar.
Haka kuma ana sa ran Buhari da shugabannin majalisun biyu za su tattauna kan batun kasafin kudin shekarar 2017 da har yanzu ba a zartar da shi ba.
Wata shida kenan bayan da shugaban kasa ya mikawa majalisar daftarin kasafin kudi amma har yanzu majalisun biyu sun gaza amincewa da shi ya zama doka.
Tuni wasu masana tattalin arziki suka shiga nuna damuwa kan cewa jinkirin da aka samu na zartar da kasafin zai sanyaya gwiwar masu zuba jari daga kasashen waje.