Buhari Ya Gana Da shugabannin Hukumomin Tsaro


Shugaban kasa Mohammad Buhari a jiya Talata ya yi ganawar sirrida manyan hafsosin tsaron kasa, ministan tsaro Mansur Dan-Ali  da kuma Babagana Monguno mai bada shawara akan harkokin tsaro.

Shugaban ne ya jagoranci zaman taron da kansa.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS, Lawan Daura , shugaban riko na hukumar leken asiri ta kasa NIA, Arab Yadum da kuma wakilin babban sifeta janar na yan sandana Najeriya.

Manyan hafsosin tsaron da suka kasance a wurin sun hada da Babban hafsan hafsoshin  Najeriya, Gabriel Olanisakin,Tukur Buratai babban hafsan soja, Ibok-Ete Ekwe , shugaban sojin ruwa da kuma Saddique Abubakar babban hafsan sojin sama

You may also like