Buhari Ya Gana Da Shugabannin Jam’iyun APC Da PDP 


Shugaban kasa Muhammad Buhari da safiyar yau ya gana da shugabannin jam’iyar APC mai mulki da kuma na jam’iyar adawa ta PDP.

Tawagar APC ta samu jagorancin shugaban jam’iyar na kasa John Odigie Oyegun  yayin da shugaban kwamitin riko na jam’iyar PDP Ahmad Muhammad Makarfi ya jagoranci tawagar shugabannin jam’iyar.

Taron ya gudana a babban dakin taro dake fadar shugaban kasa ta Aso Rock dake Abuja. 

Makarfi yace jam’iyarsa za ta cigaba da goyon bayan gwamnatin Buhari a kokarin da take na daga likkafar kasarnan gaba.  

Ya roki gwamnatin ta jam’iyar APC kan ta girmama hukuncin kotuna akan shari’ar cin hanci da rashawa.

Shugaban riko na jam’iyar ta PDP ya kuma roki Allah yakara bawa shugaban kasar lafiya da kuma basirar iya jagorancin kasarnan. 

Oyegun ya bayyana taron a matsayin wani abu na musamman,inda yace hakan ya nuna cewa Buhari shugabane na kowa  ba tare da nuna banbancin siyasa  addini ko kuma kabilanci ba. 

Buhari ya bayyana taron a matsayin wata manuniyya ta hadin kan kasa, inda yakara da cewa dimakwaradiya na bukatar jam’iyun adawa, a   cewarsa hakan ba yana nufin gaba da kiyayya ba. 

Shugaban kasar ya kuma godewa yan Najeriya kan addu’ar samun sauki da suka yi masa. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like